Hon.Babawo Ya kara ɓallo datsi a ƙaramar hukumar Sabon Gari


Hon.Babawo Ya kara ɓallo datsi a ƙaramar hukumar Sabon Gari 

Daga Idris Umar, Zariya

Wata sabuwar rikici ta kunno kai a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna, sakamakon rikicin cikin gida da ke kara ta’azzara a jam’iyyar APC.

Alamomi sun nuna cewa rikicin da ke tsakanin bangarori biyu zuwa Uku a jam’iyyar a karamar hukumar na kara kamari, alamu sun nuna ɓangarorin  kowa na kokarin kawar da abokin hamayyarsane domin cimma muradunsa na siyasa.

Lamarin ya bayyana a fili ne a lokacin da iyalan tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Hon. Annur, suka dawo jam’iyyar APC domin bayar da gudummawarsu ga jam’iyyar.

A yayin taron, Hon. Garba Datti Babawo ya yi kakkausar suka ga tsohuwar gwamnatin Ƙaramar Hukumar Sabon Gari wacce Hon. Injiniya Ibrahim Usman ya shugabanta a baya, inda ya zarge ta da almundahana da kwace kadarorin al’umma.

Daga cikin zarge-zargen da Hon. Babawo ya yi, akwai batun sayar da filin wasa da al’umma ke karuwa dashi musamman matasa da tsohuwar gwamnatin ta yi tare da sayar da shi. Ya bayyana cewa shugabannin yanzu za su yi bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an dawo da filin domin amfanin jama’a.

Hon. Babawo ya kuma yi Allah-wadai da abin da ya kira dabi’ar almundahana irin ta tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, yana mai cewa al’ummar Sabon Gari sun fuskanci irin wannan hali a karamar hukumar su. Ya bayyana fatan cewa yadda Allah Ya tona asirin tsohon Ministan Shari’a, haka ma zai tona asirin duk wadanda suka kwashe kadarorin karamar hukumar suka mallaka wa matansu da ’ya’yansu.

Ya kara da cewa sun samu rahotanni na cewa wasu daga cikinsu na shirin ficewa zuwa wata jam’iyya. Don haka, ya ja hankalin ’ya’yan jam’iyyar APC da su guji dabi’un da ka iya janyo rarrabuwar kai a jam’iyyar kamar yadda sauran sukai masu a lokacin baya.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari dangane da wadannan zarge-zarge, amma abin ya citura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Binciken wakilinmu ya nuna cewa kalaman Hon. Babawo sun shafi wani babban jigo a siyasar yankin wanda a baya bai cika mayar da martaniba amma wata majiya ta tseguntawa manema labarai cewa a wannan lokacin kowa ya shirya bayanansa na kare kansa don haka shi wanda ake harbin shima zai sako nashi bamabaman ba da jimawaba.

Post a Comment

0 Comments