Daga Idris Umar Zariya
Fitaccen matashin ɗan siyasa daga ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna, Hon. Abdullahi Alllow Maigana, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Dan Majalisar Tarayya domin wakiltar mazabar Soba, Maigana a ƙarƙashin jam'iyyar NDC a halin yanzu.
Da yake zantawa da manema labarai, Hon. Abdullahi Allow ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa NDC ne domin samar da sabon salo na siyasa da zai kawo ci gaba ga al'ummar ƙaramar hukumar Soba.
Ya ce ya shafe shekaru da dama yana fafutukar siyasa, inda ya taɓa tsayawa takara tare da riƙe mukamai daban-daban a jam'iyyar PDP. Sai dai ya ce lokaci ya yi da za su samar wa kansu sabuwar hanya ta samun ci gaba.
A cewarsa, sun gaji da wahalhalun da al'umma ke ciki, kuma burinsu shi ne samar da ci gaba mai ɗorewa ga jama'a.
Hon. Abdullahi ya bayyana cewa idan Allah Ya ba shi nasarar cin zaɓe, zai mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga matasa, inganta ilimi, kiwon lafiya, tsaron rayuka da dukiyoyi, tare da bunƙasa noma da kiwo, waɗanda su ne ginshiƙan tattalin arziƙin ƙaramar hukumar Soba.
Har ila yau, ya yi alkawarin tallafa wa mata tare da ba su damar taka rawa a harkokin ci gaban al'umma, yana mai cewa ba zai manta da gudunmawar da suke bayarwa ba.
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kasance jakadu nagari na jam'iyyar NDC, su riƙa wayar da kan jama'a cikin lumana da gaskiya kan manufofin jam'iyyar.
Haka kuma, ya buƙaci matasa da su zauna lafiya tare da mara wa jam'iyyar NDC baya domin tabbatar da sauyin da al'ummar Soba ke fata.
A nasa jawabin, shugaban jam'iyyar NDC na ƙaramar hukumar Soba, Hon. Yayo, ya ce kamar yadda suka yi aiki tukuru a baya, haka za su ci gaba da jajircewa domin ganin jam'iyyar ta samu nasara.
Ita ma shugabar mata ta jam'iyyar NDC a ƙaramar hukumar Soba, Molina Jonathan, ta ce mata da maza a yankin sun shirya tsaf domin mara wa jam'iyyar baya saboda manufofinta na kawo ci gaba da inganta rayuwar al'umma.
Ta yi kira ga matan ƙaramar hukumar Soba da su fito su goyi bayan Hon. Abdullahi Allow domin tabbatar da wannan buri.
Shi ma shugaban matasan jam'iyyar NDC na ƙaramar hukumar Soba, Abubakar Raiyanu, ya tabbatar da cewa matasa za su bai wa Hon. Abdullahi Yallow cikakken goyon baya, yana mai cewa sun gamsu da kyawawan manufofinsa da kudurorinsa na ci gaban al'umma.
0 Comments