SIRRIN FARIN CIKIN IYALI
Daga Amina Yusuf Gwamna,Kano
MIJI YA KAWO, MATA TA SARRAFA
Abinci mai inganci yana taimakawa jiki da kare jikin daga cututtuka. Lafiyayyen abinci ba wai iya lafiya ya ke ginawa ba. Yana gina kauna, hadin kai da mutuntaka a gida. Miji Ya kawo halal dai-dai karfinsa. Mata ta sarrafa ba ganda, korafi, ko mita.
Kai jama'a maza na kokarifa !
Anyiwa kura ruwa wani irin mummunan Lodi, Buhunhuna masu nauyin gaske . Turata ya ke yi da kyar ga shi tsakiyar rana ce amma Sauri ya ke ta kokarin yi ahaka. Ya samu yin sawu dayawa , abiya shi ya samu kudin cigaba da ciyar da iyalansa. Na tausaya ma sa matuka. Duk da ya kammala digirinsa, aikine ba'a samu ba. Bai zaunaba, yana aikin Gini, ranar da ba aikin Gini ya taho kasuwa . Bawan Allah har da Dako! Ya dage da neman halal domin samar da abinci ga iyalansa ba tare da sakaci ba. Ya dage yai Arziki domin ya fada aji agidansa. Ya dage ya zama tsani arabu da talauci da har iyayensa sai sun huta. Yai arziki da zai warware matsalarsa , ta iyalansa da sauran al'umma.
Wadata iyalinka da abinci, mahadin abinci, ruwa da sauransu shi ne babba abinda zai kare martabar Sarautarka a gidanka. Kuma ka na da lada Mai girma kamar yadda ya zo a Hadisi.
Annabi SAW ya ce "Dinarin da ka kashe akan iyalinka, da Dinarin da ka bayar ga miskini, da dinarin.... , Mafi girma daga cikinsu shi ne wanda ka kashe akan iyalinka".
Muslim
Abin takaici ne yadda na ga mata na barin maza da yunwa! Mata sai ganda, yawo da girman kai ba girki agida. Nai sauri na ce" wasu mata ba! . Ta ce duk matan kano! Raina Ya baci sosai, na kule karshe, Hajiya ba ki yi adalci ba.
Ta dinga mita tana ta bala'i. Na ce"Yanzu idan na ga kuskure awajen 'yar gombe 3/4, sai ince duk matan Gombe?". Hajiya ta ce " Nayi shekaru da fara kasuwanci, kowanne wata zanzo kano in sari kaya. Duk zuwana yan kasuwa da na ke gani. A kasuwa suke karyawa, anan za su ci na rana. Wasu ma 5-6pm sai sun ci kafin su bar kasuwa. Mu kuwa, Da Asuba muke girkawa mazanmu abincin Kari, kuma mu sa musu na rana su tafi dashi kasuwa.
Mai da wukar!
Mu kuma mazanmu 'yan boko ne, sai mun karya tare su fita aiki. Da rana su ci agida, in su na gida, da dare mu ci tare. Mu awajen matan kano Soyayya da abinci suna da alaka mai karfi. Ance "Hanya mafi sauki na mallakar Miji ita ce ta cikin cikinsa ".
Malama Ban yarda da ke ba!? To me ya sa wadanda na ke gani kullum cikin sayen abinci?
Hajiya wani watakila ba ya wadata gidansa da abinci. Sai ya gwammace alallaba na gidansa. Yayin da in ya fita sai shi ya ci abinda ya ke so. Kuma za a iya samun wanda ya wadata gidan , yai rashin dace matarsa ne. Ba ta damu da mai zai ci ba.
Motarmu ta wuce Birnin kudu, sai aka tsaya ayi sallah aci abinci kafin mu wuce Gombe. Gidan da muka shiga mu ka samu kyakkyawa mace , tana ta hura wuta icce, tai sharkaf da gumi. Can gefe ga surfe ta zuba ga kuma yara 2 na kuka. Muna fitowa hajja Gana ta ce wanna fa yarinya ce Sosai, ba ta kai Ashirinba. Kalli ke kyace tai shekara 40 . Wancan zuwa ta bamu labarinta, abin tausayi. Miji ne in ya tafi nema, ba aike har sai ya dau watanni. Wahala ce ta mai da ta haka!
MATAKAI NA KORE YUNWA A GIDAJENMU:
HAKURI
Koyawa iyali tarbiyya ta addini, yadda zamu dinga rayuwa da wadatuwa da abinda Allah Ya bamu. Koyawa iyalanmu Dukkan ladubban cin abinci. Biyawa yara tarihin Annabi (SAW) da na sahabbansa.
Sai akwana arbain agidan Annabi ba a dora murhuba. Suna cin dabino da ruwa.
Koyawa iyalanmu azumi nafila.
Kasa cikinmu kashi 3. Daya ruwa,daya abinci, daya kuma Iska.
Koyawa iyalanmu Kyauta da sadaka musamman na Abinci. Musulunci yana karfafa a raba abinci da juna da kuma yin hakuri da abinda ake da shi.
Annabi SAW ya ce " Abincin mutum guda yana wadatar da biyu. Abincin mutum biyu yana wadatar da hudu. Abincin mutum hudu yana wadatar da takwas".
GODIYA:
Koyawa iyalanmu fadin Alhamdulillah kan dukkan Niima da muka samu. Da basu labarai na irin wahalar da wasu ke ciki ( ba sa iya samun abinci) .
Mace ta dinga yabo da godewa mijinta kan dukkan dawainiyarsa.
Miji ya dinga sa albarka ga dukkan hidimar gida, da duk Abinci da matarsa ta dafa. Mu dinga tunawa Alkawari Allah ne cewa " Idan ku ka Gode , lalle zan kara Muku ( Niima) amma idan ku ka kafirce, to azabana mai tsanani ne". Sura:14 :7.
ALKINTA KAYAN ABINCI
Yana da muhimmanci a ilmantar da iyali kan yadda za'a rage asara da yadda za'a ciyar da gida cikin basira.
1- Tanadar kayan abinci, cefane na mako-mako ko wata -wata. Lokacin Arharsu (kaka).
2- Zuba su a mazubi: Kamar robobi
3- Dafa Iya abinda ake da buqata.
4- Girki da gwaji ( Measurement).
5- Gama Abinci akan lokaci, kafin iyali su galabaita.
A karshe yana kyau mu canja tunaninmu , idan kida ya canja, rawa ma sai ta canja.
A irin wannan kasa tamu, da irin yanayi tsada rayuwa. Yana da kyau Mazaje su hada Aiki, kiwo da kasuwanci.
Idan Ka ta so aiki, ka je shago , alokacin damuna ka na Noma.
Mata su koyi Sana'a ko kasuwanci.
Iyaye su dora 'ya'yansu a sanaoi da kasuwanci.
Mazaje su karfafi mata da 'ya'yansu da jari.
Ciyarwa ta zama ba, rowa, ba mako, ba karya, ba alfahari, ba kiwa, ba gundura.
Ma'aurata su dinga tuna hidimar da sukewa juna, Miji ya kawo, mata ta sarrafa fa ibada ce. Kuma Sirrin farin ciki iyali. Mu roki Allah Ya hore kuma Ya sa mana albarka.
0 Comments