Dallatun Zazzau ya amsa kiran shugabannin ƙananan hukumomi na tsayawa takara a shiyya ta ɗaya


Dallatun Zazzau ya amsa kiran shugabannin ƙananan hukumomi na tsayawa takara a shiyya ta ɗaya

Daga Idris Umar, Zariya

A yau ne shugabannin ƙananan hukumomi na shiyya ta ɗaya a jihar Kaduna suka kai wata ziyara ta musamman ga tsohon gwamnan jihar, Dakta Muktar Labaran Yaro, inda suka roƙe shi da ya tsaya takarar kujerar Sanata mai wakiltar shiyya ta ɗaya ( zone one) ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

Tawagar shugabannin, wadda shugaban ƙungiyarsu a jihar Kaduna, Hon Abubakar Jamilu Albani Samaru, ya jagoranci fara taron a offishin Hon Jamilu Ahmed (JAGA), kafin daga bisani su tafi zuwa gidan tsohon gwamnan da ke unguwar Kaura a cikin birnin Zariya.

Da isarsu, bayan gabatar da manyan baƙi, mai masaukin baki Hon Jamilu Ahmed (JAGA) ya ba shugaban tawagar damar bayyana manufar zuwan tasu ga tsohon Gwamnan da jama'ar dake wajan taron.

A jawabinsa, Hon Abubakar Albani ya bayyana cewa sun zo ne bisa wakilcin al’ummar shiyya ta ɗaya domin roƙon Dakta Muktar Labaran Yaro da ya fito takarar Sanata, bisa da la’akari da irin kwarewa, mutunci da kuma halayen kirki da yake da su.

Ya ƙara da cewa irin waɗannan halaye ne suka sa suka ga ya dace su zo kai tsaye su gabatar masa da wannan roƙo nasu.

Da yake mayar da martani, tsohon gwamnan ya fara da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, sannan ya gode wa shugabannin ƙananan hukumomi, ‘yan majalisa da sauran ‘yan jam’iyyar APC da suka halarci taron.

Ya bayyana cewa yana matuƙar farin ciki da irin ƙaunar da aka nuna masa, tare da bayyana cewa a duk tsawon rayuwarsa ta siyasa, bai taɓa neman muƙami da kansa ko da kuɗinsa ba, illa al’umma ce ke kiransa.

Daga nan ya amince da roƙon da aka yi masa, tare da neman addu’ar al’umma domin samun nasara, da kuma damar yi wa jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya hidima.

Daga cikin waɗanda suka yi jawaban roƙo kafin amincewarsa akwai shugaban ƙaramar hukumar Kudan, Hon Dauda Iliya sai mai masaukin baki Hon Jamilu Ahmed (JAGA) da Barrista Hajiya A’isha Muhammad.

Taron ya samu halartar dimbin magoya bayan jam’iyyar APC maza da mata.

A ƙarshe, Hon Yakubu Soja ne ya gabatar da jawabin godiya bisa karɓar roƙon da tsohon gwamnan ya ya batare da jin wani tsoroba.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments