Yan Bindiga Sun Matsawa Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jihar Kadun



Daga Idris Umar, Zariya

Kungiyar maharba ta ƙasa mai suna United Hunters Association of Nigeria ta bayyana cewa hare-haren ’yan bindiga na ƙara tsananta a Giwa Local Government Area da ke cikin Kaduna State.

Shugaban kungiyar na ƙasa, Malam Taju, ya bayyana wa manema labarai cewa mambobin kungiyar sun yi gumurzu da ’yan bindiga a wurare daban-daban a yankin a cikin satin da ya gabata.

Ya ce a yayin artabun, ’yan bindigar sun harbi daya daga cikin mambobin kungiyar, wanda yanzu haka yake kwance a asibiti yana karɓar magani.

A cewarsa, artabun ya faru ne sakamakon matsin lambar da kungiyar ke yi wa ’yan bindigar ba dare ba rana. Ya kara da cewa a wani gumurzu da suka yi da su, sun samu nasarar kwato wasu kayayyakin da aka sace daga hannun ’yan bindigar.

Shugaban ya yi kira ga gwamnatin Katsina State da Kaduna State da su kara tallafawa kungiyoyin sa-kai irin tasu da kayan kariya domin karfafa tsaro a yankunan karkara.

Ya jaddada cewa duk da rashin tallafi daga gwamnati, kungiyar za ta ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Malam Taju ya kuma gode wa jami’an tsaro, musamman rundunar sojoji da ’yan sanda, da kuma al’ummar yankin da ke ba su hadin kai wajen gudanar da ayyukansu.

A nasa bangaren, daya daga cikin mambobin kungiyar da aka harba mai Suna (Sarki Lurwanu) ya tabbatar da cewa ’yan bindigar sun ji masa rauni a cinyarsa bayan artabu a wani gari da ke cikin yankin, amma yana samun sauki cikin ikon Allah.

Shi ma sakataren kungiyar, Comrade Ibrahim Isa Ahmad, ya bayyana cewa hare-haren ’yan bindiga na kara tsananta musamman a Giwa Local Government Area.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su rika bai wa kungiyar rahoton duk wani mutum da suke zargin baƙo ko wanda ba su yarda da shi ba domin taimakawa wajen inganta tsaro.

A ƙarshe, ya roki gwamnati da ta kara duba halin da kungiyar ke ciki da kalubalen da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya kare Nigeria baki daya.

Post a Comment

0 Comments