Daga Abubakar Musa, Kaduna
Shugaban EBIRAN Zazzau, Alhaji Lawal, ya yabawa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambassador Dakta Ahmad Nuhu Bamalli, bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya a Masarautar Zazzau da ma Jihar Kaduna baki ɗaya.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin bikin hawan Bariki na bana, wanda aka gudanar bayan kammala bukukuwan Karamar Sallah. Ya yi wannan bayani ne bayan ya sauka daga kan dokinsa, a yayin da sarakuna, jami’ai da shugabannin kabilu suka yi wa Sarkin Zazzau rakiyar girmamawa kamar yadda al’ada ta tanada.
Alhaji Lawal ya nuna matuÆ™ar jin daÉ—i da yadda Majalisar Masarautar Zazzau ke bai wa wakilan kabilar EBIRA kulawa da girmamawa a kowane lokaci. Haka kuma, ya yi kira ga al’ummar EBIRA da su mara wa Sarkin Zazzau baya domin Æ™arfafa haÉ—in kai da zaman lafiya tsakanin al’ummomi daban-daban.
Bugu da Æ™ari, Sarkin ya yi fatan alheri ga Mai Taimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna da Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, tare da addu’ar Allah Ya ba su ikon gudanar da bukukuwan Sallah cikin koshin lafiya.
An gudanar da bikin hawan Bariki ne kwana guda bayan Sallar Karamar Sallah, inda Sarkin Zazzau ya hau doki daga cikin gari zuwa filin Polo da ke GRA Sabon Gari. A wajen taron, ya karÉ“i gaisuwar sarakuna da wakilan masarautarsa, tare da halartar manyan baÆ™i ciki har da jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
An gudanar da taron cikin kwanciyar hankali, inda aka fara lafiya aka kuma tashi lafiya.
0 Comments