Yadda ruwa Ya Mamaye Anguwar Barhim, Mazauna yankin sun koka
Daga wakilinmu
A yadda ake ciki mazauna unguwar Barhim da ke cikin birnin Katsina sun zargi masu aikin gina tagwayen titin da ya haɗa yankin da hanyar Eastern Bypass da rashin samar da magudanan ruwa, lamarin da suka ce ya haddasa ambaliyar ruwa a gidajensu bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a safiyar Laraba.
Mazaunan sun bayyana cewa tun kafin fara daminar bana suka yi ta nuna damuwa kan rashin gina magudanan ruwa a aikin titin, suna gargadin cewa hakan na iya jefa al’umma cikin haÉ—arin ambaliya.
A cewarsu, ruwan saman da aka yi da sanyin safiyar Laraba ya mamaye gidaje da dama tare da jawo asarar dukiyoyi sakamakon rashin hanyoyin da ruwa zai bi.
Lamarin ya haddasa damuwa ga mazauna yankin,
Mazaunan sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda da ta gaggauta ɗaukar matakan magance matsalar.
0 Comments