SHIRIN KARFAFA GWIWAR AL’UMMA NA MAI CANTER MICRO PERSONAL EMPOWERMENT SCHEME 1.0 YA SAMU KARBUWA A ZARIYA
Daga Idris Umar, Zariya
An gudanar da taron kaddamar da shirin Maicanter Micro Personal Empowerment Scheme 1.0 a harabar Sakatariyar Karamar Hukumar Zariya, inda ya samu gagarumar karbuwa daga al’umma.
Shirin, wanda Sakataren Karamar Hukumar Zariya, Hon. Alhaji Shuaibu Abdullahi Maicanter, ya assasa karkashin tafiyar jam’iyyar APC a karamar hukumar, an tsara shi ne domin tallafawa da karfafa tattalin arzikin al’umma.
Taron ya shaida rabon kayayyakin tallafi daban-daban ga sama da mutum 700 daga sassan Karamar Hukumar Zariya.
Daga cikin kayayyakin da aka rabawa wadanda suka ci gajiyar shirin akwai motoci, babura, kekuna, injinan gyaran tayoyi (vulcanizing machines), injinan dinki, buhunan wake, galan-galan na man gyada, da kuma tallafin kudi ga zababbun mata.
Haka kuma, an rabawa masu bukata ta musamman kekunan guragu domin saukaka musu zirga-zirga da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Bugu da kari, wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin sun samu guraben tallafin karatu, abin da ya kara jaddada muhimmancin ilimi a matsayin ginshikin ci gaban mutum da al’umma.
Har ila yau, an ware guraben Umrah guda goma ga wasu daga cikin mahalarta shirin, domin ba su damar gudanar da wannan ibada mai albarka tare da kara bunkasa tasirin shirin ta fuskar addini da zamantakewa.
Taron ya nuna kyawawan dabi’u na tausayi, hadin kai da kuma jajircewa wajen ci gaban al’umma daga tushe. Mutane da dama sun bayyana cewa wannan kokari ya yi daidai da salon shugabancin Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, wanda ke ci gaba da ba da fifiko ga shirye-shiryen bunkasa tattalin arziki, ilimi da walwalar jama’a.
Irin wadannan shirye-shiryen na taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci, samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Ta hanyar zuba jari a rayuwar jama’a, al’umma na samun damar dogaro da kai da kuma zama masu amfani ga kasa baki daya.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron tare da gabatar da jawabai akwai Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Jihar Kaduna (ALGON), Hon. Abubakar Jamil Albani Samaru, Hon. Baba Isa da kuma Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Hon. Jaga.
A jawabansu, sun yaba wa Hon. Mai Canter bisa wannan gagarumin aiki tare da nuna cikakken goyon bayansu gare shi.
Sun kuma gode wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da Mai Girma Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon. Abbas Tajuddeen, bisa kokarin da suke yi wajen ci gaban al’ummar Zariya da kasa baki daya.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin mota ya bayyana godiyarsa tare da cewa wannan tallafi zai kara masa kwarin gwiwa wajen gudanar da harkokinsa da inganta rayuwarsa.
Haka kuma, Hajiya Aisha, wadda ta samu tallafin kudi har Naira 300,000, ta yaba da kokarin Hon. Maicanter wajen tallafawa al’umma da inganta rayuwar jama’a.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Hon.
Maicanter ya gode wa Allah Madaukakin Sarki tare da jinjinawa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, Mai Girma Abbas Tajuddeen da kuma Shugaban Karamar Hukumar Zariya bisa goyon bayan da suke ba shi.
Ya ce da yardar Allah zai ci gaba da gudanar da shirye-shiryen da za su amfani al’umma, tare da fatan alheri ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da sauran shugabannin jam’iyyar APC a matakai daban-daban.
An gudanar da taron cikin nasara, inda aka fara lafiya aka kuma tashi lafiya.
0 Comments