TARON GOYON BAYAN YAN TAKARKAUN JAM’IYYAR APC A KARAMAR HUKUMAR SABON GARI

Daga Idris Umar Zariya 

A Yau Laraba, 13th May 2026, mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari Kuma Shugaban ALGON Na Jihar Kaduna, Hon. Sheikh Jamil Abubakar Albani Samaru Zaria tare Da Sauran Manyan Jiga-Jigan Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) A Fadin Karamar Hukumar Sabon Gari, Sun Bayyana Cikakken Goyon Bayansu ga Hon. Sadiq Ango Abdullahi Domin Ci Gaba Da Wakiltar Mazabar Sabon Gari Federal Constituency A Wa’adi Na Biyu.

Wannan Muhimmin Goyon Bayan Ya zo ne bisa Jagoranci Da Amincewar Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Senator Uba Sani, Wanda Ya Nuna Cikakken Yarda Da Nagartar Wadannan Shugabanni Da Kuma Ayyukan Alherin da Suke gudanarwa domin Cigaban Al’umma da Jam’iyya baki daya.

Kamar yadda taron ya gudana ya tabbatar da nuna goyon Bayan da amincewa da mutane kamar haka.

Mai Girma Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu GCFR Domin Wa’adi Na Biyu.

Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Domin Wa’adi Na Biyu.

Dr. Mukhtar Ramalan Yero  Domin Takarar Sanatan Kaduna State Zone One Senatorial District.

Hon. Sadiq Ango Abdullahi Domin Wa’adi Na Biyu A Matsayin Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Sabon Gari Federal Constituency.

Hon. Sani Dahiru Basawa Domin Wa’adi Na Biyu A Matsayin Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Mai Wakiltar Basawa Constituency.

Hon. Nasiru Idi Kano A Matsayin Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Mai Wakiltar Sabon Gari Constituency.

Hakika wannan hadin kai da goyon bayan ya Nuna Karfin Jam’iyyar APC A Karamar Hukumar Sabon Gari da Kuma Yunkurin Cigaba da Samar da Nagartaccen Jagoranci a Dimokuradiyya, da Ayyukan raya Kasa.

Kuma anyi Addu’ar Allah Ya Kara Basira, kikima, Lafiya, Da Nasara Ga Wadannan Shugabanni domin Su Samu Cikakkiyar Nasara A Zabe mai zuwa. Allah Ya Basu Ikon Cigaba Da Bautawa Al’umma da Gaskiya, Adalci, da kishin kasa.

Abin da wannan taro ya kunsa ke nan an tashi lafiya da fahimtar juna.

Post a Comment

0 Comments