Daga Idris Umar, Zariya
Professor Muhammad Sani Bello ya gudanar da wani taron gaggawa tare da shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress na Shiyya ta Ĉaya, mai Ĉunshe da mazabu 87 da Ĉananan hukumomi 8, a Ĉaramar hukumar Sabon Gari da ke jihar Kaduna.
An gudanar da taron ne a babban Éakin taro na Dove Center da ke Kwangila a Zariya, inda aka haÉa manyan shugabanni da mambobin kwamitin zartarwa (EXCOs) na jam’iyyar ADC daga Zone One baki Éaya.
Taron ya mayar da hankali wajen Ĉarfafa haÉin kai tsakanin shugabannin jam’iyyar tare da tsara dabarun yakin neman zaÉe gabanin zaÉen fidda gwani (Primary Election) da za a gudanar a ranar Litinin, 25 ga Mayu, 2026.
Haka kuma, taron ya jaddada kudirin jam’iyyar na samar da ingantaccen shugabanci tare da wayar da kan shugabanni kan wasu matsaloli da ake zargin suna faruwa a cikin jam’iyyar ADC a faÉin jihar Kaduna.
A jawabinsa, Mainan Zazzau ya bayyana cewa manufar taron ita ce samar da haÉin kai da daidaito a cikin jam’iyyar, tare da neman goyon bayan shugabanni domin tabbatar da nasararsa wajen zama Éan takarar gwamna guda Éaya na jam’iyyar ADC a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa Farfesan ya bai wa shugabannin jam’iyyar na mazabu 87 da ke Zone One amanar kuri’arsa tare da neman amincewarsu kai tsaye.
Daga cikin manyan baĈin da suka halarci taron akwai:
Aliyu Makarfi, Daraktan Kamfen
Gambo SakadaÉi
Murja Abdul Hasan, Shugabar Mata ta Zone One
Haka kuma, daga cikin malaman addinin da suka halarci taron akwai Sheikh Surajo Bomo.
An gudanar da taron lafiya kuma an tashi lafiya.
0 Comments