Hon Nasiru Idris ya lashe zaben fidda gwanin a mazaɓarsa ta Sabon Gari


Hon Nasiru Idris ya lashe zaben fidda gwanin a mazaɓarsa ta Sabon Gari

Daga Idris Umar Zariya 

A ranar Laraba 20 ga watan Mayun 2026 ne aka gudanar da zaben fadda gwani a Jamɓiyar APC a fadin jihar Kaduna baki daya.

Karamar hukumar Sabon Gari tana daga cikin karamar hukumar da ta marawa zaben baya.

Ƙaramar hukumar Sabon Gari tana da  mazabu 11 tare da yan majalisu guda biyu da suke wakilta su a kujerun majalisar jihar Kaduna ta gudanar da zaben ta Kamar haka.

A gundumar Basawa akwai Hon. Sani basawa wanda ya lashe zaben shi ba hamayya kamar yadda malamin zaben Hon. Ubale Ali Baba ya shelanta cewa duniya bayan kammala zaben yace Hon Sami Basawa ya sami Kuri'u 174 wanda hakan ya bashi damar kashen zaben a wannan lokaci.

Gundumar Sabon Gari Hon Nasiru Idris shine ɗan takara da Abokin takararsa Hon Bashir Zango

A yayin da aka gama lissafa kuri'ar da ta fito daga mazabu guda 7 kamar  Dogaraw da Hanawa da Zabi sai Cikaji da Anguwar Gabas da Jushi.

Kamar yadda malamin zaben ya shelanta wa Duniya cewa Hon. Nasiru Idris ne ya sami kuri'a 853

Shi kuma abokin takararsa Hon. Bashir Zango Ya sami Kuri'u 278

Malamin zaben Hon. Abubakar Umar, (Yarima) ya bayyana Hon. Nasiru Idris a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin a mazaɓar Saboda Gari.

Post a Comment

0 Comments