KO BAYAN RASUWAR TA: YADDA TARBIYYAR MAHAIFIYATA KE CI GABA DA HASKAKA RAYUWATA
Marubuciya Amina Yusuf Gwamna Kano
Ta na bani litattafai in karanta, sai kuma ta dan tsakuro wani abu daga ciki tai bayani. Ta ban Zaman Aure a Musulunci, Annabi Dan Gatan Allah, Tarihin Sahhabai da sauransu. Ina jin dadi nan da nan in karanta in dawo da shi.
A wancan lokaci, wata rana gaba na yai ta faduwa, na cika da tsoro, sanda na kalli littattafai da ta miko min :"Ilimin Shimfida Musulunci da Gishirin Ma'aurata." Cikin bacin rai ta ce" Ki karanta tsaf zan miki tambayoyi a kowanne Babi."
Nai dakinmu da sauri, kamar ba zan iya karantawaba. Na karance su tsaf , sai na rasa ta ina zan fito balle mu hada ido, saboda tsananin kunya.
Wannan shi ne sila ta rubuce-rubuce na da Nasara ta Nasihar Aure.
Tarbiyya na nufin a gina yaro a hankali, ta kowanne bangaren rayuwarsa. Mai tsarkakakkiyar Zuciya, mai kyawawan halaye, mai lafiyayyen jiki, mai ilimi.
*MATAKAI YADDA TARBIYYA ZA TA GINA MIJI DA MATA:*
GINA HALAYE: Koyawa 'ya'ya ladabi, gaskiya, kunya, godiya.
ADDINI: koyar da Addini da tsoron Allah zai sa Miji da Mata kokarin kulawa da hakkoki juna bisa adalci.
WARWARE SABANI: Ba zagi ko mummuna tashin hankali.
JURIYA: koya musu jure kalubale ba tare da rabuwa ba.
KAUNA: Tasirin kauna wajen sa natsuwa a Aure.
NASIHAR AURE: Sanya 'ya'ya Maza da mata zuwa Horo, bita na Aure . A tabbata anga shaida kamar yadda ake sa akawo shaida asibiti kafin Aure.
ABUBUWA DA NAI GADO AWAJENTA
Soyayya Annabi (SAW)
Son Al'qur'ani
Kula da Marayu
Hakuri yayin musiba
Zumunci
Mai da lamari ga Allah Yayin da kaddara
Son makota .
Ba da guddumawa wajen warware matsaloli jama'a.
Kyauta/ Sadaka.
Hajiya Mama ta rero wadannan baituka daga Wakar Cutar So Ba ta da Magani. Cikin littafin Dausayin Soyayya.
Ina sauraronta ina kallon shafi. Mama ta ce tun dacan yabo da nuna kauna ta hanyar waka ba bakon abu ba ne.Hatta acikin tatsuniya akan samu wakokin soyayya.A yanzu cigabanki shine, ki dinga iya shirya ma mijinki rubutacciya takarda da sakonni Soyayya akai-akai. Na farko Ki dinga ribata tayashi farin cikinsa da kulawa , alokuta na musamman. Sallah, Azumi, ranar Aurenku ( Anniversaries) da sauransu.
Ki sa wa ranki tunani alkhairai mijinki, sai ki yi ta kara sonsa. Har ki dinga jin soyayyarsa ibada ce. In ki kai Nasara jin kaunarsa amatsayin ibada , komai zai dinga zuwa miki da sauki.
Alamun cikar Imani mutum shine tsantsan soyayyarsa ga Allah Subhanahu. Duk abinda za ka yi, ka yi don Allah.
Annabi SAW ya ce:"Wanda yai soyayya dan Allah, kuma ya bayar don Allah, kuma ya hana don Allah to hakika imaninsa ya cika" (Tirmizi)
In ka na son misalai na kauna mai Daraja to ka duba ire iren hadisai na rayuwar Annabi SAW da Assayida Aisha (RA).
Aisha ta ce "Annabi SAW Yana kishingida akan cinyata, Alhali ina haila, sai ya karanta Qur'ani." (Bukhari)
Cikin horewa ta Allah(SWT) sai shawarwarinta su kai tasiri sosai. Mun shaku dashi matuka, kullum ana tare. Ban zata ba, Ya wuce tunani na. Allah Ya karbi rayuwarsa. Tashin hankali Ya wuce misali."
Alhamdulillahi ala kulli haalin! Juriya da yin abinda ya dace ya samu saboda tunano yadda ta ke yi mini, duk lokaci wata jarrabawar da ta same ni. Misali: Mama sai ta ce" Ki dauko Qur'ani ki lizimci karantawa. Ki yi ta sallah kina addua. In shaa Allahu za ki samu sanyi aranki, kuma za ki samu mafita, komai zai warware."
Idan ta ga na kasa yi da gaske, sai ta fara mita: Kin san dai bana yawon malamai ko!? Daga yau in kin canja, nima in tayaki addua. Idan ba za ki yi ba, nima na huta.
Allah Ya Gafartawa Hajiya Mama ,da irin wannan tarbiyya tata, na samu hasken da ke haskaka min da zarar na shiga duhu.
Kafin in kammala , Ba kyawun fuska ke sa aso mutum din-din ba, kyawun hali ne ke sa Kauna ta dawwama a zuciya. Soyayya ta gaskiya tana da bukatar Aiki, hakuri da sadaukarwa. Koyawa 'ya'ya Soyayya zai raya Aurensu cikin kulawa, da Nishadi.
0 Comments