Daga Amina Gwamna Kano
Duk wacce za'a raka dakinta na Aure sai na ji ana ta nanata ma ta " ki yi hakuri" Da wanna na fahimci dole sai kin iya ba da hakuri alokacin da ke ki kai laifin ,da iya ba da hakuri kan laifin da ba ki yi ba ( karbar uzuri ba tare da neman Uzuri ko zargin wani ba.
Bada Hakuri yana gyara dangantaka cikin sauqi, za ka yi magani matsala, saki, yaji, kiyayya da gaba. Mahassada ba za su samu kofar shiga tsakaninku ba.
Alhaji a matsayinka na shugaba kar ka daukewa matarka wuta ka yarda ace akai tsawon lokaci ba ku sulhunta ba. In ba za ka iya ba ta hakuri da kalmomi ba. Rungumarta ba ta hakuri ne, Sumbantarta ba ta hakuri ne. Yabon kwalliyarta ko shigar ma ta da kyautar bazata duk ba ta hakuri ne.
Ni kam ba zan iya irga adadin sabani da muka samu ba. Alhamdulillah!
Babba Nasarata,
ina iya hakuri in jure fushinsa da rigimarsa ba na kula shi ( No matter what zaman Aure na buqatar girmamawa ko da rai ya baci ) Miji dai shugaba ne, hakuri dashi ibada ne . Shi kuma Gani yadda na ke bashi hakuri sai Ya zama in har ya fahimci na yi fushi mai sunan fushi to ba zai taba biye minba yai fushi zai ta bani hakuri , ba zai sauraraba sai ya tabbatar na huce ko na hakura. Kunga Asshe ke ma ki na ta ka rawa koya ma mijinki mutunta al'amuranki.
Amma ai nima ina da kurakuraina sai dai dukkan mu muna mutunta junanmu komenene ya faru. Bama yadda muyi fushi wai muyi fada ana gaba balle fadi in fada, ban san wanna ba.
Daga cikin kuskure da Ma'aurata ke yi, shine komai akai min, sai na rama . Ba da hakuri na nuna girmamawa . Na fassara ki na mutuntashi a matsayin mijinki. Jama'a muna mantawa fa, hakuri ibada ne za ka samu lada, kai siffa ce mai daraja.
Allah Ya na cewa " Lalle ne masu hakuri za'a cika musu ladansu ba tare da lissafi ba.
Zumar:10
Idan soyayya ka ke son bawa kariya kar ta gushe, to ka fahimci yaren bada hakuri guda 5.
👉 Bayyana nadama
👉 Karbar laifi
👉 Kokarin gyara abinda aka lalata.
👉 Canja Hali
👉 Bada Hakuri
Ataqaice is normal ku samu sabani, kowa ya na da irin na sa ajizanci. Wata ma adole haka za ka rayu da ita. Kawai ku mayar da hankali wajen fahimtar junanku da yin hakuri. Ance Mai hakuri ya kan dafa dutse har ya sha romonsa.
0 Comments