Bashir Sakadaɗi ya koma Jam'iyar ADC


Bashir Saka daɗi ya koma Jam'iyar ADC

Daga Idris Umar Zariya 

A yau ne aka gudanar da bukin komawar Honorable Bashir Sakadadi Zuwa Jam'iyar ADC.

An gudanar da bikin karɓar katin shaidar zama cikakken ɗan 
jam'iyyar ADC ne bayan
ya sauya sheƙa daga Jam'iyar PDP mai alamar Lema a Masallaci Idi dake Dogara ta ƙaramar hukumar Sabon Gari Zariya.

Hon. Sakadadi, wanda ya riƙe muƙamai daban-daban, 
ciki har da Shugabancin Ƙaramar Hukumar Sabon Gari kuma ya taba rike matsayin Adviser a Gwamnatin jihar Kaduna, kuma tsohon Kwamishina ne a Jihar Kaduna, 

Ya samu tarba mai armashi daga shugabanni da kuma mambobin jam'iyyar ta ADC.

Honorable Usman Ibrahim tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ya halarci wannan gagarumin biki, domin nuna goyon baya da maraba ga Honorable Bashir Sakadadin

Dubban mutane ne suka halacci taron tare da nuna jin ɗadinsa.

Dukkan mayan bakin sunyi kira ga matasa dasu tashi tsaye wajan bayar da tasu gudummawar.

Kuma taron anyi shi lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

0 Comments