ABUBUWA 3 DA YAKAMATA MA'AURATA SU SANI


ABUBUWA 3 DA YAKAMATA MA'AURATA SU SANI

Daga Amina Yusuf Gwamna 

" Ki yi Aure...." Kowanne iyaye damuwarsu dai 'ya'yansu mata har mazanma su yi Aure. 

Menene Aure? 
Aure Yarjejeniya ce tsakanin Namiji da Mace da zasu rayu da juna, su taimaki juna bisa iyakantaccen tsarin  zama tare da aka sanya musu hakkoki da wajibabbun abubuwa da suke tsakanin Ma'aurata n. ( Muhd Abu Zahr ).

Babban matsalar da ke rugurguza gidajen Ma'aurata, shine iyaye ba sa mayar da hankali agino Tarbiyyar wadannan abubuwa guda 3.

TARBIYYAR RUHI:  A koyama Ma'aurata yin ibada da kusanci da Allah ( SWT). Kokari sallah, addua, azumi, da karatun Al'qur'ani. 

A koya musu yadda za su tsabtace zuciyarsu. Ba hassada, kiyayya ko girman kai. 

A koya musu Hakuri da Tawakkali. Wannan zai saukaka musu Yarda kaddara da za ta same su cikin sauki ,ba tare da samun ciwo ( depression) , ko sabawa Allah ba.  

Allah Ya lillibe mahaifana da  iyayen musulmi duka da RahamarSa. Alhamdulillah! Da bamu samu wannan tarbiyya ba,  da irinmu dayawa yanzu muna Dawanau. Mata na samun jarrabawa iri-iri miji Ya kwanta jinya, Ya samu karayar Arziki ko wacce miji zai sake ta . Idan akwai Tarbiyyar Ruhi, zuciyar mace na samun natsuwa da karfin jure wahalhalu da suka same ta. 
Madallah da iyayen da sukai ma 'ya'yansu wannan tarbiyya. 

TARBIYYAR JIKI:
A koya ma maaurata 
Kulawa da jikinsu tun kafin su yi Aure. Cin abinci mai gina jiki, shan ruwa sosai. Motsa jiki.

Sassafe na kan ganshi da kayan atisaye, mu kan je filin sukuwa mu dan zazzaga. Bayan samun lafiya na kanji nishadi akowacce fita irin wannan. Irin haka yakamata Ma'aurata ku dinga fita yin atisaye tare, musamman ki ka ga mijinki ya na da kiba kuma yana yawan jinya. 

Hutu da barci: Mafi yawan ' Yan Mata da Samari ba sa samun isasshen bacci saboda wayoyinsu. 
Wata yarinyar haka za ta cigaba da wanna dabiar ko da ta yi Aure. 
Namiji da bai san muhimmanci hutu da barci ba, ya tauye ma kansa sirrin jin dadin Aurensa. 

Allah Ya sanya mana ladduban shiga gida 'ya'yanmu ne ko wasu in har sun balaga. Ko daki  bayan anyi sallama sai 'ya'ya sun  nemi izini da cewa " in shigo?" 

Acikin Suratul Nur: 58 .Allah (SWT) yana nuna cewa akwai lokuta uku na sirri ga Ma'aurata. 
1- Kafin Asuba 
2- Lokacin hutun rana (qailula).
3-Bayan Isha'i.

Jikinki wajen hutawar mijinki ne, muddin ba kya shiryawa haka to fa ba zai dinga zuwa ba.
 


TARBIYYAR LOKACI:
Allah Ya na cewa 
2-Lalle ne mutum Yana cikin hasara. 
Suratul Asr .

Baya halatta ga mutum wani lokaci ya wuce shi bai san amfanin da ya sama wa kansa acikin wannan lokacinba. 


A koya ma Ma'aurata  tsara lokaci. Misali yin jadawal abinda za su yi a sati ( 1 week). Sannan yin abubuwa da farawa da abinda ya fi amfani ( priorities). 

Annabi (SAW) ya ce " Ni'imomi biyu mutane dayawa suna yin asara acikinsu: lafiya da kuma lokaci. 
( Bukhari) 

Kyakkyawan amfani da lokaci zai ginawa Ma'aurata rayuwa mai albarka.

A karshe Sirrin Aure mai
 Dorewa shine inda aka samar da Ma'aurata dukka su na da Ruhi mai karfi, lafiyayyen jiki da tsara abubuwa domin alkinta lokacinsu. Wannan gidan za su zama masu cikakken Nasara a duniya da lahira. Yadda za'a ja Mace ajiki a ba ta wannan tarbiyya, haka yakamata abawa Namiji . 

Wallahu A'alam

Post a Comment

0 Comments