Shugaban karamar hukumar Sabon Gari ya kaddamar da aiyukan gyaran makarantu masu yawa karkashin shirin (ROOSC) a ƙaramar hukumar Sabon Gari
Daga Idris Umar, Zariya
Jihar Kaduna — Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari kuma Shugaban kungiyar shugaban kananan hukumomi na jihar Kaduna a Nigeria wato (ALGON) Sheikh Jamilu Abubakar Albani, ya kaddamar da aikin sake gina da kuma gyaran wasu zababbun makarantu a wasu gundumomi na ƙaramar hukumar ta Sabon Gari.
An miƙa ayyukan ga ‘yan kwangila domin su fara aiki nan take, kuma ana gudanar da su ne a ƙarƙashin shirin Reaching Out-of-School Children (ROOSC) — wani shirin inganta ilimi na gwamnatin jihar Kaduna da nufin inganta kayayyakin makarantu da kuma faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi ga yara.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin, shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa wannan shiri muhimmin mataki ne wajen ƙarfafa tsarin ilimi da samar da muhalli mai kyau ga ɗalibai domin bayar da ilmi a fadin ƙaramar hukumar.
Ya kuma nuna matuƙar godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, bisa jajircewarsa wajen magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma fifita bunƙasa fannin ilimi a jihar ta Kaduna.
A cewarsa, ayyukan za su taimaka matuƙa wajen inganta yanayin koyarwa da koyo tare da ƙarfafa yara shiga makaranta don samun ci gaba..
Makarantun da Za a Gina da Gyara sun hada kamar haka.
Za a gina sabon ginin Junior Secondary School a Anguwan Fulani, cikin harabar Army Children School a Jushi Ward.
Za a gina sabon Junior Secondary School a garin Gwanda.
Kuma za a gyaran LEA Primary School, Anguwan Makeri, Basawa Ward.
Kuma za a aikin gini a makarantar Tsangayar Malam Jibrin Musa, Kurmin Bomo.
Kuma cikin ikon Allah za a gyaran makarantar Saidu Model Primary School, Samaru.
Shugaban ya buƙaci al’ummomin da ke yankunan da za su amfana su ba ‘yan kwangila cikakken haɗin kai tare da tabbatar da zaman lafiya domin ayyukan su kammala cikin lokaci.
Ya kuma jaddada cewa al’umma su zama masu bayar da hadin kai a dukkan wajan da ake gabatar da ayyukan.
Wannan shiri na nuna ƙoƙarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi na inganta ilimi da ƙarfafa jama'a akan karatun yara a jihar Kaduna baki ɗaya.
Shugaban yace gwamnati, ta tabbatar da cewa kowane yaro yana da damar samun ilimi mai inganci.
Shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki a fannin ilimi a siyasa ce da mazauna yankin da suka halarci taron sun yaba da wannan mataki, suna masu cewa saka hannun jari a ilimi na nufin saka hannun jari a makomar matasa a ƙaramar hukumar Sabon Gari.
Malamai sarakuna dukkan manya da suka halacci wannan waje sun yabawa mai girma Gwamnan jihar Kaduna tare da yin masa fatan Allah ya maimaita kujerar sa da magoya bayansa.
0 Comments