Jagoran Islamic Movement in Nigeria, Ibraheem Yaqoub Zakzaky, ya bayyana cewa shi da mabiyansa ba barazana ba ne ga Nigeria, yana mai cewa a maimakon haka su ne mafita ga matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Malamin ya yi wannan bayani ne a cikin wani saÆ™on bidiyo da aka wallafa a shafin Tafsir Da Jawaban Jagora, inda ya jaddada cewa manufarsu ita ce kawo gyara da mafita ga al’umma, ba tare da haifar da wata barazana ga Æ™asar ba.
A cikin saƙon, Sheikh Zakzaky ya ce:
Mu ba barazana ba ne ga ƙasar nan, mu ne mafita ga ƙasar nan.
Rahoton ya fito ne daga shafin Tafsir Da Jawaban Jagora, wanda ke wallafa tafsiri da kuma jawaban malamin ga mabiyansa a lokuta daban-daban.
0 Comments