Ana zaton rasa rayuka masu yawa bayan tashin Bom a Meduguri


Ana fargabar an yi asarar rayuka da jikkatar da dama sakamakon tashin Bom a Kasuwar Monday Market dake Maiduguri bayan Sallar magribar yau Litinin.

Rahotannin sun bayyana cewa jim kadan bayan fashewar na kasuwar, sai kuma aka jiyo tashin wasu a Tashar Bama da kuma Post Office dake Ahmadu Bello Way a Maidugurin.

Muna tafe da karin bayani.

Post a Comment

0 Comments