🟢 YANZU YANZU: Sheikh Zakzaky ya miƙa saƙon ta’aziyya kan kisan Malam Yahaya Masussuka.
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya miƙa saƙon ta’aziyya kan kisan babban malamin Alƙur’ani, Alaramma Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka.
An kashe Malam Masussuka tare da wani baƙonsa a ƙofar gidansa da ke Dutsen Ma, a ranar Litinin.
A cikin saƙon ta’aziyyar, Sheikh Zakzaky ya bayyana kisan malamin a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi, la’akari da gudummawar da ya bayar wajen yaɗa ilimi, tarbiyya da kira ga zaman lafiya.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ɗalibansa da sauran al’ummar Musulmi, tare da roƙon Allah Ya karɓe shi a matsayin shahidi, Ya kuma saka masa da Aljanna.
Sheikh Zakzaky ya kuma yi addu’ar Allah Ya tozarta waɗanda suka kashe malamin da waɗanda suka mara musu baya.
0 Comments