SHUGABAN KASAR IRAN YACE; ZUWA TARON MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA DAMA CE DON IRAN TA BAYYANA MATSAYINTA GA DUNIYA BAKI ƊAYA!


SHUGABAN KASAR  IRAN YACE; ZUWA TARON MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA DAMA CE DON IRAN TA BAYYANA MATSAYINTA GA DUNIYA BAKI ƊAYA

Daga idis Umar, Zaria 

Shugaban Kasar  Iran Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UN General Assembly) na ba Iran damar mai  muhimmanci don isar da saƙonta kai tsaye ga kasashen duniya baki ɗaya!

Pezeshkian ya nuna cewa:  Wannan taro na ba Iran "dama ta musamman"  don bayyana matsayinta da damuwoyin ta a gaban wakilan kasashen duniya gaba ɗaya

Iran na son duniya ta ji  gaskiyar abin da ke faruwa ba ta hanyar kafofin watsa labarai na yamma kawai ba Tehran na shirye don tattaunawa da kowane ɓangare da ke son zaman lafiya bisa gaskiya da adalci.

Wannan sanarwa ta Pezeshkian na da matuƙar muhimmanci — domin a lokaci da Amurka ke ƙoƙarin ware Iran daga kasuwancin duniya da takunkumai — Iran na amfani da babban taron duniya wajen isar da saƙonta kai tsaye ba tare da tace ba!

Taron Majalisar Ɗinkin Duniya na ba duk ƙasa — ko maniya ko ƙarama — damar tsayawa a fili ta bayyana ra'ayinta ga duniya — wanda Iran ke ganin dama ce da ba za ta bar ta ta wuce ba!

Iran na tafiya UN — duniya za ta ji matsayinta — gaskiya za ta bayyana a gaban dukkan kasashe!  Duniya na jira saƙon Iran!

Truth News Hausa

Post a Comment

0 Comments