An bainaya Irin TELA Maize a matsayin mafi inganci a cikin Irin masara a Zariya 

Daga Idris Umar, Zariya

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Samaru, Zariya, ta halarci Ranar Nuna ingancin TELA Maize da aka gudanar a ranar Asabar, 29 ga Agusta, 2026, Æ™arÆ™ashin taken “Cin Sa Shi Ne Shaida” (Eating Is Believing).

Taron ya haÉ—a manoma, masu bincike, abokan hulÉ—ar ci gaba, sarakunan gargajiya, wakilan kafafen yaÉ—a labarai da sauran masu ruwa da tsaki, domin wayar da kan jama’a kan fa’idodi, inganci da kuma yadda za a yi amfani da TELA Maize cikin aminci.

Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da Ci gaba, Bincike da ƘirÆ™ire-Æ™irÆ™ire, Farfesa Aliyu Sanusi Rafindadi, ne ya jagoranci taron.

A jawabinsa, Farfesa Rafindadi ya jaddada muhimmancin ƙirƙire-ƙirƙire a fannin noma, haɗin gwiwa da amfani da ingantattun fasahohi wajen ƙarfafa samar da abinci, ƙara yawan amfanin gona da kuma inganta rayuwar manoma.

ÆŠaya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a wajen taron shi ne ziyarar filin noman TELA Maize, inda mahalarta suka samu damar ganin yadda nau’o’in masarar ke gudanar da rayuwa a Æ™arÆ™ashin yanayin gonaki na zahiri.

Nau’o’in TELA Maize na da wasu muhimman siffofi, ciki har da jure fari da kuma jure Æ™warin fall armyworm da stem borers, waÉ—anda ke daga cikin manyan Æ™alubalen da ke addabar noman masara.

Waɗannan siffofi na taimakawa manoma wajen rage asarar amfanin gona tare da samun kariya daga wasu manyan ƙwari da ke lalata masara.

Dangane da taken taron, “Cin Sa Shi Ne Shaida,” an bai wa mahalarta gasasshiyar masara, dafaffen masara da kuma masa da aka yi daga TELA Maize.

Wannan gwaji kai tsaye ya ba mahalarta damar dandana kayayyakin da aka sarrafa daga TELA Maize tare da ƙara fahimtar fasahar da ke tattare da irin masarar.

Haka kuma, an ƙarfafa mahalarta da su dogara da shaidar kimiyya da abin da suka gani da kansu, maimakon jita-jita, wajen fahimtar wannan fasaha ta noma.

Daga cikin waÉ—anda suka gabatar da jawabai a wajen taron akwai Shugaban Manoman Jihar Kaduna, Alhaji Nuhu Aminu, wanda ya bayyana cewa ya noma TELA Maize da kansa kuma ya samu riba fiye da abin da ya saba samu a baya.

Alhaji Nuhu Aminu ya tabbatar da ingancin irin masarar, inda ya yi kira ga manoman Jihar Kaduna da ma na sauran sassan ƙasar da su rungumi wannan fasaha tare da yin amfani da irin TELA Maize domin ƙara yawan amfanin gona da samun riba.

Ya kuma yi kira ga gwamnatoci da su tallafa wajen samar da irin TELA Maize ga manoma, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen bunƙasa noma da ƙara arzikin ƙasa.

Shi ma Farfesa Rabi’u Adamu, É—aya daga cikin masu bincike da suka bayar da gudummawa wajen Æ™irÆ™ira da bunÆ™asa wannan nau’in masara, ya bayyana muhimmancin TELA Maize ga manoma da Æ™asa baki É—aya.

Farfesa Rabi’u Adamu ya tabbatar wa mahalarta cewa TELA Maize ta samu ingantaccen tsarin bincike na kimiyya, tare da kira ga manoma da su yi amfani da ita ba tare da tsoro ko shakku ba, bisa bayanan kimiyya da aka tabbatar.

Haka kuma, Shugaban Cibiyar Nazarin Albarkatun Ƙasa ta Ƙasa (NEARLS), Farfesa Yusuf Ahmed Sani, ya bayar da tabbaci tare da ƙarfafa gwiwar manoma kan amfani da TELA Maize, yana mai jaddada muhimmancin rungumar sabbin fasahohin noma domin inganta samar da abinci.

Daga cikin manya mahalartan taron akwai Market Development Manager na Hybrid Seed, Mista Ojo Olewale, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma.
Ranar Nuna TELA Maize ta samar da muhimmiyar dama wajen ilmantar da manoma, haÉ—a kan masu ruwa da tsaki, gudanar da gwaje-gwaje a gonaki da kuma wayar da kan jama’a bisa hujjojin kimiyya.

Taron ya kuma ƙara haskaka irin damar da TELA Maize ke da ita wajen haɓaka yawan amfanin gona, ƙarfafa samar da abinci da kuma inganta rayuwar manoma.

An gudanar da taron lafiya, sannan aka tashi lafiya.