ABUTH Zaria Ta Horas da Ma’aikatan Lafiya 70 Kan Gano Ciwon kansar Mazakunta a Zariya


Daga Idris Umar, Zariya

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH), Zariya, ya gudanar da wani taron horaswa kan cutar kansar mafitsara ta maza (prostate cancer), inda aka horas da ma’aikatan kula da lafiya na al’umma (Community Health Extension Workers – CHEWs) guda 70 daga cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 35 da ke ƙananan hukumomin Giwa, Sabon Gari da Zariya na Jihar Kaduna.

An gudanar da taron a ranar Juma’a, 28 ga Agusta, 2026, da nufin ƙara wa ma’aikatan lafiya ilimi da ƙwarewar da za su taimaka wajen wayar da kan al’umma da kuma gano cutar kansar mafitsara ta maza tun da wuri.

Taron ya gudana ne tare da haɗin gwiwar African Research Group for Oncology (ARGO) NCAT Scholars, Memorial Sloan Kettering Cancer Center (MSKCC) da ONCOCLINICS.

Manufar horaswar ita ce bai wa CHEWs ilimi da dabarun da suka dace wajen wayar da kan jama’a, gudanar da bincike, gano mutanen da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar, gano alamomin cutar da wuri, da kuma tura waɗanda ake zargin suna ɗauke da cutar zuwa asibitocin da suka dace domin samun ƙarin kulawa.
Masu shirya taron sun bayyana cewa ana sa ran mahalarta za su yi amfani da ilimin da ƙwarewar da suka samu wajen ƙarfafa al’umma su rika zuwa asibiti da wuri, inganta hanyoyin tura marasa lafiya, da kuma taimakawa wajen yaƙi da cutar kansar prostate a cikin al’ummominsu.

Daga cikin waɗanda suka jagoranci horaswar akwai Dakta Musliu Tolani, Dakta Ismail H. Zubairu, Dakta Dalhat K. Sani, Dakta Aminu Bello Liman, Abdulkareem Kabir da Dakta Shehu Salihu Umar.

A ƙarshen taron, an bai wa mahalarta takardun shaidar kammala horaswar.

Wasu daga cikin mahalartan sun bayyana godiyarsu bisa damar da aka ba su ta samun horaswar, tare da bayyana ƙudurin yin amfani da ilimin da suka samu wajen inganta ayyukan kiwon lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da kuma cikin al’ummominsu.

Muhimmancin Gano Cutar da Wuri
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa cutar kansar prostate na daga cikin cututtukan da ke shafar maza, musamman yayin da suke ƙara shekaru.

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke ƙara haɗarin kamuwa da cutar shi ne tsufa, musamman a tsakanin maza masu shekaru masu yawa.

Daga cikin alamomin da ka iya nuna matsalar prostate akwai samun jini a fitsari, wahalar yin fitsari ko toshewar hanyar fitsari, yawan yin fitsari, da kuma wasu matsaloli yayin yin fitsari.

Masana kiwon lafiya sun yi kira ga maza da su rika zuwa asibiti domin duba lafiyarsu musamman idan sun lura da irin waɗannan alamomi, maimakon jiran cutar ta tsananta.

Haka kuma, idan mutum ya lura da jini a cikin fitsari ko kuma yana jin zafi ko wahala yayin yin fitsari, ana ba shi shawarar ya garzaya asibiti domin samun cikakken bincike daga ma’aikatan lafiya.

Kiran ABUTH ga Jama’a
A cewar bayanan da aka tattauna yayin horaswar, jinkirin zuwa asibiti na daga cikin matsalolin da ke kara haddasa tsanantar cututtuka, yayin da wasu mutane kuma kan fara amfani da magungunan gargajiya kafin su nemi kulawar asibiti.

Wannan na iya sa a samu jinkiri wajen gano cutar da kuma fara maganin da ya dace.

Saboda haka, an yi kira ga maza da sauran jama’a da su kasance masu kula da lafiyarsu, su rika zuwa asibiti da zarar sun lura da wasu alamomin da ba su saba gani ba, ba tare da jiran ciwo ya tsananta ba.

Taron ya kasance cikin nasara, inda mahalarta suka tashi lafiya bayan kammala shirin horaswar.

Post a Comment

0 Comments